An kashe wani limamin a garin new york,limamin mai suna Maulanta Akonjee.Shi dai Imam Maulama Akonjee yana kan hanyarsa ta zuwa gida tare da abokinsa Tharam Uddin jiya Asabar, bayan an idar da sallah, sai wani ya harbe su a ƙeya.
Musulmi dake yankin da lamarin ya auku sun ce, kisan na nuna ƙyama ce, kuma suka ɗora alhakin lamarin akan ɗan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump.
Sun ce, Trump ne ya haifar da yanayi na matuƙar ƙiyayya ga musulunci.
Amma ya zuwa yanzu 'yan sanda sun ce, ba a tantance dalilin aikata kisan ba.
Kuma ba a kama kowa ba dangane da aikata kisan.
Yan sandan birnin New York na Amurka sun ce, suna bincike dangane da
kisan wani mai wa'azin addinin musulunci da abokinsa a unguwar Queens.
Title :
An Kashe Wani Limamin Massallaci A New York
Description : An kashe wani limamin a garin new york,limamin mai suna Maulanta Akonjee.Shi dai Imam Maulama Akonjee yana kan hanyarsa ta zuwa gida ta...
Rating :
5