A kalla mutane shidda ne ake fargabar sun mutu a cikin wani tashin hankali da ya faru a garin Mafara na jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya.
Lamarin ya soma ne a cikin wata kwaleji da ke garin inda dalibai musulmi suka ce wani dalibi da ba musulmi ba ya yi batanci ga Annabi Muhammadu (SAW), amma kuma sai rikicin ya bazu zuwa ciki gari.
A yanzu dai an girke jami'an tsaro da suka hadar da sojoji da 'yan sanda dan tabbatar da doka da oda.
Bayanai na cewa hankula sun kwanta, sai dai an rfue kwalejin sakamakon tashin hankalin.
Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar tashin hankalin, sai dai ta ce tana gudanar da bincike.
Title :
An Kashe Mutane Shida A Zamfara, Bayan Anyi Batanci Ga Annabi Muhammadu (SAW)
Description : A kalla mutane shidda ne ake fargabar sun mutu a cikin wani tashin hankali da ya faru a garin Mafara na jihar Zamfara dake arewa maso yammac...
Rating :
5