Daga Jaridar Rariya
Rundunar 'yan sanda a jihar Legas sun rufe wasu gidaje 12 a titunan Abeokuta da Ibadan da ke yankin Ilasamaja bayan da aka gano rijiyoyin da aka gina don satar Man dizil mallakar kamfanin mai na kasa(NNPC).
Da yake karin haske kan batun, Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Steve Ayorinda ya nuna cewa gidajen da abin ya shafa duk na haya ne kuma masu gidajen ne suka haka rijiyoyin ta yadda suka fasa bututun da man dizil din ke bi inda ake janyo wa ana sayar wa jama'a.
Ya kara da cewa an dauki matakin rufe gidajen ne saboda hadarin da suke da su ga al'umma inda ya ce an aje motar kashe gobara a yankin don gudun ko ta kwana. Ya kara da cewa tuni an kama mutane uku da ke da hannun a cikin badakalar
Source Rariya
Title :
An Gano Gidaje 12 A Legas Da Aka Tona Rijiyoyi Don Satar Mai
Description : Daga Jaridar Rariya Rundunar 'yan sanda a jihar Legas sun rufe wasu gidaje 12 a titunan Abeokuta da Ibadan da ke yankin Ilasamaja bayan...
Rating :
5