A jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya, wani jami'in hukumar Alhazan jihar ya damfari wasu maniyyata Hajjin bana su kusan 30 kudin kujerunsu.
A halin da ake ciki dai maniyyatan sun ce suna cikin tashin hankali, kasancewar ba su ga sunayensu a jerin alhazan jihar da ake sa ran za su fara tashi zuwa Saudiyya a karshen wannna makon ba.
Daya daga cikin maniyyatan, Mallam Yunusa Waziri ya shaida wa BBC cewa jami'in shi ne shugaban ma'aikatan hukumar Alhazan, kuma duk shekara yakan sayar da kujeru ga maniyyata.
A cewarsa, ta hannun jami'in suka yanki fom din hajjin, kana suka bude asusun ajiya, inda kowannensu ya fara da naira 700,000 kana daga bisani suka cika zuwa naira miliyon daya da dubu hamsin.
Maniyyatan sun ce nemi jami'in sama da kasa amma ba su gan shi ba, kuma sun tuntubi Hukumar alhazan domin su san makomarsu, amma ta ce su nemi hakkinsu a wajen jami'in.
Sai dai Hukumar Alhazan jihar Nasarawa, a nata bangaren ta ce tana da labarin jami'in, wanda ta bayyana shi da cewa bara-gurbi ne, kuma ta fara gudanar da bincike a kan lamarin.
Sai dai ta ce ba za ta dauki alhalkin batan kudin maniyyatan ba, kasancewar ba a hannunta suka danka shi ba.
Yanzu dai jami'an tsaro sun bazama neman jami'in da nufin gurfanar da shi a gaban kuliya.
Title :
An Damfari Maniyyatan Jihar Nasarawa
Description : A jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya, wani jami'in hukumar Alhazan jihar ya damfari wasu maniyyata Hajjin bana su kusan 30 kudin kuj...
Rating :
5