Daga Shafin VOA
A daidai lokacin da Uba Ahmed Nana ke ganawa da shugabannin jam'iyyar APC domin lalubo zaren warware rikicin jam'iyyar a jihar Bauchi, matasa sun yi dafifi suna nuna rashin amincewa da gwamnansu
Uba Ahmed Nana yace tun farko jam'iyyarsu ta kuduri anniyar zama da 'yan majalisar dokokin jihar Bauchi da 'yan majalisar tarayya da suka fito daga jihar da kuma shi gwamnan jihar.
Yace bayan sun gama wannan zama na daidaiku zasu yi zama na hadin gwuiwa baki daya kuma zasu cigaba da yin hakan duk bayan wata ukku domin su rufawa kansu asiri.
Uba yace duk dan jam'iyyar APC na halal idan gwamnatin APC nada matsala zama ake yi tare a tattauna ba'a shiga kasuwa ba.a baza koli.
Amma a daidai lokacin da Uba Ahmed Nana ke ganawa da shugabannin jam'iyyar domin neman masalaha akan rikicin APC a jihar ta Bauchi sun yi dafifi a harabar wurin taron suna ihun nuna rashin goyon bayansu ga gwamnan jihar tasu Barrister M. A. Abubakar.
Galadima Abba Itas da ya jagoranci matasan yace taro ne na nuna irin halin da mutanen Bauchi suka tsinci kansu a ciki.Yace Allah ya hadasu da shugaba mara tausayi wanda ba kasar ce a ransa ba.
Yace a jihar an kwashe wata biyar zuwa shida babu albashi. An hana ma'aikata albashinsu kana wasu sun rasa rayukansu. Haka ma 'yan fansho ba'a basu kudadensu ba. Bugu da kari an kori ma'aikata barkatai babu wani dalili. Hatta hakimai an koresu.
Sabo Muhammad mai ba gwamnan jihar Bauchi shawara a harkokin labarai cewa yayi tsakaninsu da Ubanguji idan wannan watan ya cika shi ne za'a bisu albashin wata biyu, sai malaman kananan hukumomi dake bin albashin wata ukku.
Title :
Al'ummar Bauchi Sun Gamu da Shugaba Mara Tausayi-Matasa
Description : Daga Shafin VOA A daidai lokacin da Uba Ahmed Nana ke ganawa da shugabannin jam'iyyar APC domin lalubo zaren warware rikicin jam'iy...
Rating :
5