Daga Mashkur Ibrahim Excellency
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa matasa bisa hadin kai da goyon bayan da suke bawa Gwamnatinsa na irin addu'oin da fatan Alheri da sukeyiwa Gwamnatinsa a shafukan intanet.
Ganduje yayi wannan jinjinawar ne a cikin jawabinsa da ya gabatar a wajen bikin zagayowar ranar matasa ta duniya da ya gudana a filin wasa na Sani Abacha, dake Kofar Mata a birnin Kano wanda Daraktan Yada Labarai na fadar Gwamnatin jihar, Salihu Tanko Yakasai ya fitar,
Gwamnan yana mai cewa "irin wannan halacci da matasanmu ke nuna mana ya kara mana kwarin guiwa wajen yin ayyukan da zai amfanesu duk kuwa da matsin tattalin arziki da kasarnan ke fama dashi. A cikin shekara Guda, munyi ayyukan da ya shafi matasa kamar haka :
Mun koyar da matasa 250 a fannin kimiyya da fasahar Sadarwa (ICT training) sannan muka basu kayan aiki;
Mun koyar da matasa 100 gyaran motoci a cibiyar gyran motoci na PAN Learning Centre dake Kaduna;
Mun kai mata 60 kasar Turkiyya sun koyi fasahar likitancin dasa kwayar halitta;
Gwamna Ganduje ya cigaba da bayyana cewa "mun kuma dibi matasa 742 a shirin bunkasa fannin Noma muka basu babura da zasu rika amfani da su wajen safarar abinci zuwa cikin gari;
Mun kuma samar tare da rabawa manoma wadanda galibi matasa ne injinan ban-ruwa guda 5000 wadanda mafi yawa a kyauta suka samu.
Sai dai Gwamnan ya nuna damuwarsa bisa yadda aka baro matasan Kano a baya a fannin wasu sana'o'in dogaro da kai wanda hakan yasa Gwamnatinsa ta tashi tsaye wajen ganin an cike wannan gurbi. A inda Gwamnatin jihar ta hada hannu da ofishin mataimakin shugaban kasa a fannin bunkasa sha'anin sana'o'i domin ganin matasan Kano sun amfana da duk wani shirin koyar da sana'o'i da Gwamnatin tarayya zata shirya misali shirin N-power da za'ayi kwanan nan.
Gwamnan yana mai cewa sun kuma tura matasan Kano 2000 domin sanya su a sabuwar hukumar tsaro ta Peace Corp, da Gwamnatin tarayya ta amince da ita kwanan nan. kuma Gwamnati zatayi dawainiya da su kama daga cinsu da shansu da situra da wajen kwanansu har su gama kafin daga bisani a dauke su aikin din-din-din a ma'aikatar harkokin cikin gida.
Bugu da kari, Gwamnan ya ce kawo yanzu kwamitin da ya kafa domin karfafawa masu kananan san'o'I, sun fara aiki tukuru domin kawo yanzu an fitar masu da Naira Milyan N132 domin aiwatar da shirye-shiryen karfafawa masu kananan sana'o'i 5000. Kazalika kwamitin na cigaba da nazarin wasu hanyoyin samar da ayyukan yi ga matasa.
Sauran ayyukan da Gwamnan yayi sun hada da samarwa da matasa 5000 aiki a kamfanin MTN da Bankin Diamond.
A karshe Gwamnan yayi kira ga sauran kungiyoyi masu zaman kansu da kamfanoni su taimakawa Gwamnati wajen kauda talauci ta hanyar karfafawa masu kananan sana'o'i domin Gwamnati kadai ba zata iya ba.
Yana mai shawartan matasa da su kasance masu son zaman lafiya da bin doka da Oda a matsayinsu na shuwagabannin gobe.
Daga cikin abubuwan da akayi a wajen bikin sun hada da wasannin motsa jiki da mika lambobin yabo da fareti daga kungiyoyin matasa daban-daban da dai sauransu.
Title :
Abubuwan Da Na Yiwa Matasan Jihar Kano A Cikin Shekara Daya -Ganduje
Description : Daga Mashkur Ibrahim Excellency Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa matasa bisa hadin kai da goyon bayan da suke bawa G...
Rating :
5