Daga jaridar Rariya
A'isha Wakil wadda rundunar sojoji ta bayyana neman ta ruwa a jallo a jiya Lahadi ta mika kanta ga rundunar tsaron a yau a Abuja.
A'isha wacce lauya ce, tana daga cikin mutane uku da sojojin ke nema bisa zarginsu da alaka da Boko Haram.
Lauyar ta ce bayan ta isa kofar hedikwatar tsaron, ta bayyana musu cewa ta kawo kanta ne saboda ana nemanta, amma jami'an tsaron dake wajen sun bayyana mata cewa ba su san da labarin ba, amma sai ta bukaci da su shiga kafafun sadarwa na gidajen jaridu za su ga labarin.
“Sai suka ce min za su duba labarin kafin su waiwaye ni" inji A'isha.
A'isha ta kara da cewa bayan 'yan mimtuna sai suka dawo suka karbe fasfo dinta inda suka bukaci ta dawo bayan mintuna goma.
Source Rariya
Title :
A'isha Wakil Ta Mika Kanta Ga Hedikwatar Tsaro Dake Abuja
Description : Daga jaridar Rariya A'isha Wakil wadda rundunar sojoji ta bayyana neman ta ruwa a jallo a jiya Lahadi ta mika kanta ga rundunar tsaron ...
Rating :
5