Tsohon ministan man fetur na Nijeriya kuma daya daga cikin dattawan jihar Borno, Shettima Ali Monguno ya rasu.
Ya rasu yana da shekaru 90
Idan ba a mance ba a watan Mayu na shekarar 2013 'yan kungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da shi kafin daga bisani suka sako shi.
Marigayi Monguno ya yi fice wajen bada gudumma domin gina makarantun boko da na addini tare kuma da daukar nauyin yara wajen karo ilmi.
Za a yi jana'izarsa a yau Asabar.
Title :
Tsohon Ministan Man Fetur Ali Monguno Ya Rasu
Description : Tsohon ministan man fetur na Nijeriya kuma daya daga cikin dattawan jihar Borno, Shettima Ali Monguno ya rasu. Ya rasu yana da shekaru 90 ...
Rating :
5