Kamfanin dillacin labarai na AFP ya ambato shugaban ranar Laraba yana cewa duk mutumin da ya aurar da mace 'yar kasa da shekara zai sha daurin shekara 20 a gidan yari.
Kazalika Shugaba Jameh ya ce iyayen yarinyar da aka yi wa auren wuri za su sha daurin shekara 21, sannan duk wanda ya san da labarin amma ya ki gaya wa hukumomi zai sha daurin shekara 10.
Ya kuma yi barazanar daure duk Malamin da ya daura auren wuri a kasar.
Shugaba Jameh ya yi kira ga majalisar dokokin kasar ta zartar da kudurin dokar da zai haramta auren wuri a Gambia.
Title :
Shugaban Kasar Gambia Ya Haramta Yi Wa Mata Auren Wuri A Kasar
Description : Kamfanin dillacin labarai na AFP ya ambato shugaban ranar Laraba yana cewa duk mutumin da ya aurar da mace 'yar kasa da shekara zai sha...
Rating :
5