Sen Malam Ali Wakili, yana daya daga cikin na gaba gaba wurin goyon bayan Shugaban majalisan dattawan najeriya Sanata Bukola Saraki
Sanata Ali Wakili yasa ankama Shugaban Matasan ne jiya dama wasu daga cikin matasa masu akidan Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar bauchi
Matashin mai suna Yusuf Usman da aka kama yana daya daga cikin matasan jihar bauchi masu goyon bayan Shugaba Buhari wanda a makon da ya gabata suka karrama P.A na Shugaba Muhammadu Buhari a bangaren Media wato Malam Bashir Ahmad
zuwa yanzu dai anyi belin Shugaban matasan APC na jihar bauchi amma har yanzu Comrade Yusuf Usman yana hannun yansanda a jihar bauchi kanda Sanata Ali Wakili ya nemi da akai wannan matashi gidan kurkuku kanda yanzu haka Matasa ke shirin gudanar da zanga zanga akan kama wannan matashi da Sanata Ali Wakili yasa akayi a jihar bauchi
Shidai wannan rikici tsakanin Yaran Shugaban Matasan APC na jihar bauchi da Sanata Ali Wakili, yasamo asali ne tun lokacin da matasan jihar bauchi suka fara nuna rashin gamsuwan su da goyon bayan Shugaban majalisan dattawa Sanata Bukola Saraki da Sanata Ali Wakili keyi duk kuwa da cewa mutane sun zabi wannan Sanata ne a guguwan Buhari amma daga baya Ali Wakili ya koma yana bin wata akida ba na Buhari ba
A lokacin da Matasa magoya bayan Shugaban matasan APC na jihar bauchi suka samu labarin cewa Sanata Wakili yana na gaba gaba wurin goyon bayan Saraki a lokacin ne Matasa masu goyon bayan Shugaban matasa suka fara nuna adawan su da Sanata Ali Wakili
Shi dai Shugaban matasan jamiyan APC na jihar bauchi yana daya daga cikin manya manyan magoya bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar bauchi dama arewacin najeriya
Shugaban matasan wanda akeyi masa lakabi da sunan Nasiru A Kasa A Tsare
Shugaban matasan APC na jihar Bauchi Sau dayawa ya sha jagorantan gangamin Matasa a jihar bauchi suna nuna goyon bayan su ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari
na baya bayan nan Shugaban matasan jamiyan APC na jihar bauchi ya jagoranci babban zanga zanga na goyon bayan janje tallafin man fetur da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi
Kanda Shugaban matasan a kowani lokaci ke goyon bayan manufufin Alkhairi na Shugaba Buhari.
Daga Ahmadu Manager Bauchi
Title :
Sanata Ali Wakili Yasa Ankama Shugaban Matasan jamiyan APC Na Jihar Bauchi
Description : Sen Malam Ali Wakili, yana daya daga cikin na gaba gaba wurin goyon bayan Shugaban majalisan dattawan najeriya Sanata Bukola Saraki...
Rating :
5