Ina taya dukkan 'yan Nijeriya, musamman al'umman musulmai murnar bukin wannan sallah Eid El Fitr, wanda yake a karshen azumin watan Ramadan.
Ina taya murna ga musulman Nijeriya da na dukkan kasashen duniyan murnar kammala Azumi wanda aka share wata cur ana yi, addu'o'i da biyayya ga dokokin addini.
Ina addu'a Allah Madaukakin Sarki ya saka mana a da albarka da kuma cigaba mai dorewa.
A cikin wannan buki na farinciki, na yi imani cewa musulman kwarai sun kara fahimtar asalin ma'ana da kuma amfanin rayuwa ta hanyar bin karantarwar Annabi SAW, mun koyi kasancewa masu hakuri, soyayya ga juna, kore son-kai da sauran kyawawan dabi'u yayin mu'amala da juna.
Yayin da muke sheda sallan Eid El Fitr, ina shawartar al'ummar Nijeriya da su yi aiki da wadannan darussa kuma mu godewa Allah saboda albarkatu da ya yi mana.
Mu kasance masu godiya, girmamawa da kuma kula da juna, ba tare da bambancin addini, yare, kabila ko siyasa ba, yayin da muke iya kokarin mu wajen karfafa kasar nan.
Ranar Litinin din da ta gabata a wannan sati, mataimakin shugaban kasa, kakakin majalisan wakilai da wasu jami'an gwamnati sun taya ni buda baki da wasu 'yan gudun hijira da wadansu gajiyayyu.
Kamar yadda na fada a yayin liyafar, ina so in sake yin amfani da wannan dama wajen kira ga mawadata da su tuna da 'yan Nijeriya da suke halin ni 'yasu saboda tashin hankali da 'yan ta'adda suka kakaba a yankunan su.
Ba wai ban san abunda 'yan Nijeriya ke ciki ba kuma ina so na yi amfani da wannan dama wajen jinjina wa sadaukarwar 'yan Nijeriya yayin da ake fama da kalubalen tattalin arziki da na rayuwa sannan ina dada tabbatar wa 'yan Nijeriya cewa gwamnati na tana yin iya kokarin ta wajen samar da ababen more rayuwa da ake bukata.
Zan kuma kara yin amfani da wannan dama wajen tabbatar da cewa bazamu ja baya ba wajen yaki da rashawa sannan zamu dau halatattun matakai wajen dakile wannan mummunan abu.
Ina jinjina wa dakarun sojoji da hukumomin tsaro a bisa nasarori da aka samu na fada da ta'addanci da kwato wadanda aka yi garkuwa da su sannan ina rokon goyan baya, fahimta da kuma hakuri daga dukkan 'yan Nijeriya da kasashen waje yayin da muke bin hanya mafi sauri wajen kawo karshen zagon kasa ga tattalin arziki a yankin Niger Delta sannan mu samar da mafita akan fadace-fadace dake faruwa a yankin.
Ina muku alkawarin samu sauki a nan gaba yayin da muke jin dadin karfafawar ku ga gwamnatin mu.
Barka da sallan Eid El Fitr Allah ya cigaba da yi wa kasar mu albarka.
Eid Mubarak!
Muhammadu Buhari
Yuli 5, 2016
Title :
Sakon Barka Da Sallah Daga Buhari
Description : Ina taya dukkan 'yan Nijeriya, musamman al'umman musulmai murnar bukin wannan sallah Eid El Fitr, wanda yake a karshen azumin watan ...
Rating :
5