Rikicin PDP na ci gaba da ta'azzara bayan da wata kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarni ga hukumar zabe mai zaman kanta(INEC) kan ta amince da 'yan takarar kujerar gwamnan jihohin Edo da Ondo na bangaren Modu Sheriff.
Haka ma, Mai Shari'a a kotun, Okon Abang ya haramta kwamitin riko na Jam'iyyar a karkashin jagorancin Ahmed Mohammed Makarfi da kuma sakamakon zaben fidda gwani na 'yan takarar gwamnan Edo da Ondo wanda kwamitin ya gudanar. A cikin wannan mako ne dai, wata kotun ta tsige Shugaban PDP, Modu Sheriff.
Title :
Rikicin PDP Na Ci gaba Da Ta'azzara
Description : Rikicin PDP na ci gaba da ta'azzara bayan da wata kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarni ga hukumar zabe mai zaman kanta(INEC) ka...
Rating :
5