Gwamnatin Jihar Neija ta kafa dokar hana bara a fadin Jihar wanda hakan ya sa Kungiyar Nakasassu ta yi wani zanga-zangar lumana a Minna Babban Birnin Jihar ta domin nuna rashin amincewarta da wannan Mataki da gwamnati ta dauka.
Wannan Dokar ta hana barace-arace a jihar ta shafi nakasassu masu bara a bakin titi da Masallatai da wuraren zaman al'umma da kuma almajirai kanana masu shiga gidajen domin neman na sakawa a bakin salati.
A jiya Lahadi ne dokar ta fara aikiinda aka kama al'majirai da dama.
Gwamnati ta bayyana cewa za ta ci gaba da wannan kame sai ranar da mabaratan suka daina sana'ar tasu.
Sai dai wasu daga cikin mabaratan a zanga-zangar sun jefa tambayoyi ga Gwamnatin kamar haka,
shin ya dace gwamnati ta kafa Irin wannan doka a daidai wannan lokaci da al'ummar Jihar ke halin hannu baka hannu kwarya?
Shin nakasassu ne kadai ya dace a kafa wa dokar?
Shin ba wasu masu aikata laifuffukane a jihar da ya dace Gwamnati ta kafa masu Doka ta musamman sai su kuma rashi ya zama laifi ne?
Kuma mai ya sa ba a yi masu wani tanadi ba kafin hana bara?
Masu karatu mai za ku cewa gwamnatin jihar Neija da su mabaratan?
Source Zuma Times Hausa
Title :
Photos: Kungiyar Masu Bara Sun Yi Zanga-Zangar Hana Su Bara A Jihar Neija
Description : Gwamnatin Jihar Neija ta kafa dokar hana bara a fadin Jihar wanda hakan ya sa Kungiyar Nakasassu ta yi wani zanga-zangar lumana a Minna Bab...
Rating :
5