Idan ba'a mance ba a karshen shekarar da ta gabata ne Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya kaddamar da aikin hanyar Misau zuwa Udubo wanda daga baya banyan nan gwamnan ya bada umarnin kara nisan aikin har zuwa Gamawa sannan ya hade da hanyar da za ta nufi Katagum Maikaba dake karamar hukumar Zaki.
Wannan aikin hanyar ya kai nisan kimanin kilomita dari (100) wanda hasashe ya nuna cewar mutane da dama za su amfana da wannan hanya kuma zai inganta harkokin kasuwanci.
Daga Shamsuddeen Lukman Abubakar
Mai tallafawa Mai Girma Gwamnan Jahar Bauchi akan harkokin sadarwa.
Title :
Photos: Gwamnan Bauchi Ya Kammala Gina Gadar Hardawa Dake Karamar Hukumar Misau
Description : Idan ba'a mance ba a karshen shekarar da ta gabata ne Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya kaddamar da aikin hanyar Misa...
Rating :
5