Tsohon shugaban hukumar EFCC Malam Nuhu Ribadu yaa koma jam'iyyar APC a yau Juma'a.
Malam Nuhu Ribadu ya sanar da sauya shekar nasa ne a shafinsa na Facebook, kuma ya karbi bakuncin membobin jam'iyyar dake mazabarsa ta Bako dake yankin Yola ta Kudu a jihar Adamwa.
Haka kuma ya ziyarci sakatariyar jam'iyyar domin gabatar da kansa.
Ribadu dai ya sauya sheka daga APC zuwa PDP ne a shekarar 2014.
Title :
Nuhu Ribadu Ya Koma Jam'iyyar APC
Description : Tsohon shugaban hukumar EFCC Malam Nuhu Ribadu yaa koma jam'iyyar APC a yau Juma'a. Malam Nuhu Ribadu ya sanar da sauya shekar nas...
Rating :
5