Jarumar 'yan wasan Nigerian Film Lola Alao ta canza addinin ta na kiristanci zuwa musulunci. Jarumar dai ta canza addinin nata ne a ranar Talata 19 ga watan yuli a Acadamic Of Propagation Nigeria wanda akafi sani da [ACADIP].
Jarumar har ila yau ta canza sunan ta zuwa Rhodiyat. Shugaban kungiyar Adepoju Yusuf shiya bayar da sanarwar labarin, ya kara da cewa, "godiya ya tabbata ga Allah; ku tayani yima Lola Alao (jarumar 'yar wasan Nigerian Film) murna, saboda a yau ta amshi kalmar shahada daga wajena. Kuma ta zabi Rhodiyat a matsayin sabon sunan ta. Allah ya yarda da ita amatsayin musulma, kuma yasa mata albarka akan duk wani abunda zatayi a rayuwanta, amin".
Alao dai ba itace ta farko a cikin yan wasan Nigerian Film data fara musulunta ba, akwai jaruma mai suna Lizzy Anjorin wanda ake ce mata Elizabeth Anjorin ada, ita ta fara musulinta harma taje aikin Hajji.
Title :
Jarumar Nollywoood Lola Alao Ta Musulunta
Description : Jarumar 'yan wasan Nigerian Film Lola Alao ta canza addinin ta na kiristanci zuwa musulunci. Jarumar dai ta canza addinin nata ...
Rating :
5