GWAMNA MASARI YA KOKA AKAN YADDA KATSINAWA KE KASHI ‘A KO INA’
Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari tare da gidauniyar nan ta majalisar dinkin duniya UNICEF sun koka game da karuwar yadda mutane ke bayan gida ko’ina a cikin jihar ta Katsina duk kuwa da haduran dan matsalolin dake tattare da hakan.
Gwamna Masari ya nuna damuwar tasa ne a yayin da ya karbi bakuncin tawagar UNICEF din ta jiha a gidan gwamnatin Muhammadu Buhari. Gwamnnan ya nuna rashin dacewar hakan tare da fadar illolin hakan ga lafiyar mu da hakan zai iya jawowa.
Gwamanan ya kara da cewa akwai yiwuwar gwamnatin sa ta duba yiwuwar samar da karin gidajen in kashin wa cikin jihar da kuma gyara wadan da ke akwai don jin dadin mutane.
Gwamnan har ila yau ya nuna rashin jin dadin sa game da yadda komai na gwamnati ake barin sa yana lalacewa amma na ‘yan kasuwa kuma ya kan dade ciki hadda gidajen kashin.
Haka zalika gwamnan ya bayyana cewa akwai bukatar tilas mutane su canza dabi’un su zuwa masu kyau su kuma rika duba lafiyar su da kuma tsaftar muhallinsu.
Tun farko dai shugabar tawagar ta UNiCEF a jihar Katsina Padamavathi Yedla ta bayyana cewa kungiyar su ta Sanitation, Hygiene and Water in Nigeria (SHAWN) zata maida hankali ne kacokan wajen ganin ta taimaki jihar don ganin a samu tsaftataccen muhalli.
Title :
Gwamna Jihar Katsina Ya Koka Akan Yadda Katsinawa Ke KASHI A Ko Ina
Description : GWAMNA MASARI YA KOKA AKAN YADDA KATSINAWA KE KASHI ‘A KO INA’ Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari tare ...
Rating :
5