Wani fitaccen dan siyasar Najeriya Dr Junadi Muhammad ya yi zargin cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari yana matukar nuna bambanci a mukaman da yake nadawa.
Dr Junadi ya ce shugaban kasar yana kuma kare wasu jami'an gwamnatinsa da ake zargi da hannu a cin hanci da rashawa.
A wata hira da BBC, babban dan siyasar ya ce an nunawa mutanen Sokoto da Kaduna da Abuja bambanci a nade-naden da aka yi na ministoci, yana mai cewa mutanen da aka nada ba 'yan asalin jihohin ba ne.
Ya ce abin takaici ne yadda aka bar wasu manyan shugabannin sojin kasar na baya da kuma na yanzu a binciken da ake yi na sace kudaden da aka ware na sayen makamai ga jami'an tsaron kasar.
Sai dai wasu mukarraban shugaban kasar sun shaida wa BBC cewa ba za su mayar da martani a kan wadannan zarge-zarge ba.
Title :
Buhari Yana Nuna Son Kai - Dr Junaid Muhammad
Description : Wani fitaccen dan siyasar Najeriya Dr Junadi Muhammad ya yi zargin cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari yana matukar nuna bambanci a mukaman...
Rating :
5