Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa na sane da matsalolin da talakawan kasar nan ke fuskanta yayin da ya kira shugabannin addinin Musulunci su isarwa jama’a sakon albishir na cewa al'amura za su daidaita nan ba da dadewa ba.
Shugaban ƙasar ya yi kiran haka ne yayin taron da ya yi da majalisar limaman Abuja a fadarsa jiya Alhamis, inda ya nemi limaman addini da su dinga kwantar da hankulan mabiyan su a duk fadin kasar nan, bisa la'akari da yadda ake fuskantar matsalolin tattalin arziki da tsaro.
Ya ce, shugabannin al'umma a matakai daban daban, na kokarin warware matsalolin talauci da rashin aikin yi da na tsaro da suka addabi Kasar nan.
Ya kara da cewa gwamnatin sa ta mayar da hankali ne kan bunkasa harkokin noma domin samar da ayyukan yi ga miliyoyin ‘yan Nijeriya da kuma ba kasar damar ciyar da kanta ba tare da tsoron yunwa ba.
Kodayake ana samun cigaba sosai a wannan bangare, yayin da gwamnati ke kokarin ganin samar da taki da magungunan kashe kwari da kuma samar da kyawawan tanadi don tunkarar daminar badi.
Domin ganin kowa ya ci moriyar wannan shirin, shugaban ya bayyana cewa an umarci gwamnatocin jihohi da shugabannin al’umma, a duk fadin ƙasar nan su samar da kungiyoyin hadin kai na taimakon juna al'umma, yayin da gwamnati za ta yi kokarin ganin ta taimaka da dabaru da kayan aiki, amma ba za a bai wa mutane kudi ba.
Shugaba Buhari ya kuma shaidawa shugabannin addinin kokarin da gwamnatinsa ke yi a bangaren inganta wutar lantarki a ƙasar nan. Saboda haka ne ma ya ce, kasar za ta kawo wadanda za su saka jari a harkokin wutar lantarki daga kasar Sin da wasu kasashen da kasar ke abokantaka dasu da suke son saka jari a aikin wutar da za a yi a Mambila da wasu wuraren.
Buhari ya tabbatar cewa matakan da gwamnatinsa take dauka a kan rikicin yankin Niger Delta za su kai ga dawamammen zaman lafiya.
Dangane da yakin da ya ke yi da cin hanci da rashawa da ‘yan ta’addan Boko Haram kuwa, Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa za ta dage, babu gudu babu ja da baya. “Ba mu da niyyar tursasawa kowa ko cin mutuncin wani. Adalci da tabbatar da an ba kowa hakkinsa muka sa a gaba," in ji Shugaba Buhari.
Ya sake jaddada cewa duk wanda aka samu ya saci kudin jama’a to, za a tilasta masa ya dawo da su, domin kasar na bukatar kudin.
Tun da farko, a madadin sauran limaman, shugaban majalisar limaman Abuja Dr Tajuddeen Muhammad Bello Adigun ya yaba da mulkin Buhari, musamman yaki da cin hanci da rashawa da ‘yan Boko Haram. Sannan ya jawo hankalin shugaban kan tattalin arzikin kasar, da matsalar kiwon lafiya da rashin ayyukan yi ga jama'a .
Title :
Buhari Ya Bukaci Malamai Su Kwantar Da Hankalin 'Yan Nijeriya
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa na sane da matsalolin da talakawan kasar nan ke fuskanta yayin da ya kira shugab...
Rating :
5