Zawarawa Da 'Yan Mata Dubu Goma Sun Yi Rijista
*Ina Matasan Dake Bukatar Aure Ba Kudi? Ga Dama Ta Samu
Daga Auwal Danlarabawa
Hukumar Hizba ta jihar Kano ta ce sama da zaurawa da 'yan mata fiye da dubu goma (10,000) ne suka yi rajistar neman su amfana daga tsarin nan na auren Zaurawa da 'yan mata, wanda gwamnatin jihar Kano ke shiryawa.
Masu shirya auren sun ce matakin na taimaka wa wajen rage adadin zaurawa da 'yan mata da ke neman mazajen aure.
Sai dai wannan na faruwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke kukan karancin kudin shiga. Yawancin matan da suka yi rijistar su, sun ce halin rayuwa da rashin abinda za su tare a gidan Mijinta kamar gado da katifa su ne suka sanya su shiga wannan tsari dan su samu tallafi.
Ba wannan ne karon farko da gwamnatin jihar Kano ke aurar da
zawarawa da 'yan mata ba a jihar, kuma masu kudi da 'yan kasuwa na kawo ta su gudummawar.
Title :
Ana Shirin Aure Zawarawa Dubu Goma A Jihar Kano
Description : Zawarawa Da 'Yan Mata Dubu Goma Sun Yi Rijista *Ina Matasan Dake Bukatar Aure Ba Kudi? Ga Dama Ta Samu Daga Auwal Danlarabawa Hukumar...
Rating :
5