Hukumar kasar Indonesia ta ce an zartar da hukuncin kisa ga wasu mutane hudu da aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi, uku daga cikin su 'yan Nijeriya ne.
Mataimakin babban layuan gwamnati Noor Rachmad ya ce daya mutumin dan kasar ta Indonesia ne.
Wasu rahotanni da hukumomi ba su tabbatar da su ba sun ce 'yan Najeriyar dai na cikin wasu mutane 14 da hukumomin na Indonesia suka yanke wa hukuncin kisa, kuma a kashin farko aka harbe mutane hudu cikin su har dan kasar ta Indonesia.
Tun da fari dangin mutanen sun taru domin yin bankwana da su ta karshe.
An kuma ga motocin daukar marasa lafiya guda goma sha bakwai sun nufi wajen da za a kashe mutanen, sha hudu daga motocin na dauke da makara.
An bayyana sunayen wadan da aka kashe din da suka hada da Freddy Buiman wanda dan Indonosia ne, sai kuma yan Nigeriar uku da suka hadar da Seck Osmane, da Humphrey Jefferson EJike da kuma Michael Igwhe.
Wadanda kuma suka rage suke jiran hukuncin na kisa sun hadar da wasu 'yan indonsia uku, da 'yan Nigeria biyu, da dan Pakistan da ba-indiye, da kuma 'yan Zimbabwe biyu.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty international ta yi Allah wadai da kisan, inda ta ce abu ne mai sa kaduwa, da ya saba da dokokin gida da waje.
Kasar ta Indonesia na daga kasashen da suka fi dokoki masu tsauri kan harkar ta'ammali da miyagun kwayoyi.
A bara ma an kashe masu masu ta'ammali da miyagun kwayoyoin goma sha hudu.
Shugaba Joko Widodo ya yi imanin cewa, kasar na fuskantar yawan shan miyagun kwayoyi, kuma lamarin na karuwa fiye da kima.
Wannan shi ne kisan masu safarar miyagun kwayoyin 'yan kasashen waje masu yawa da shugaba Widodo zai aiwatar tun hawansa kujerar mulki a 2014 .
Title :
An Zartar Da Hukuncin Kisa Ga Wasu 'Yan Nijeriya Guda Uku A Kasar Indonesia
Description : Hukumar kasar Indonesia ta ce an zartar da hukuncin kisa ga wasu mutane hudu da aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi, uku daga cikin s...
Rating :
5