Wata mata mai shekaru 42, mai 'ya'ya bakwai, mai suna Misis Eunice Elisha, a safiyar jiya Asabar ta gamu da ajalinta a lokacin da ta fito wa'azin Kirista a kudancin Gbazango dake garin Kubwa a Abuja, inda wasu da ba a san ko su wanene ba suka yi mata yankan rago tare da burma mata wuka a ciki.
Eunice, wacce babba ce a cocin 'Redeemed Christian Church of God', dake kan titin Old NEPA, Phase 4, Kubwa, wadanda suka kashe ta din sun bar ta kwance cikin jini da bible da wayanta a kusa da ita.
Mazauna yankin ne suka ci karo da gawarta daga bisani suka sanar da jami'an tsaro suka zo suka dauke gawarta, kafin mijinta ya zo ya gabatar da kansa.
A yayin da yake yi wa manema labarai jawabi, mijin mamaciyar, Mista Olawale Elisha wanda shi ma Fasto ne a cocin da matarsa take, ya bayyana cewa matar tasa ta shiga makwabta wa'azi ne da misalin karfe biyar na safe, amma sai labarin mutuwarta kawai ya ji.
Title :
An Yi Wata Mata Yankan Rago A Abuja A Yayin Da Take Wa'azin Kirista
Description : Wata mata mai shekaru 42, mai 'ya'ya bakwai, mai suna Misis Eunice Elisha, a safiyar jiya Asabar ta gamu da ajalinta a lokacin da t...
Rating :
5