Shugabar rikon kwarya ta Karamar Hukumar Chikun da ke cikin Jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Ladi Yahuza ta bayyana cewa Karamar Hukumar ta bankado yadda ake biyan wasu ma’akatan da suka mutu albashi.
Hajiya Hadiza Ladi Yahuza ta bayyana hakan ne a hirar ta da maneme labarai a Kaduna.
Ta bayyana cewa sun gano hakan ne, a lokacin da aka gudanar da aikin tantance ma’aikatan karamar hukumar.
“Mun gano wasu daga cikin ma’aikatan hukumar da suka mutu, kuma har yanzu akwai sunayensu a kan kundin biyan albashin karamar hukumar. Mun kuma gano wasu ma’aikatan da suka yi ritaya da kuma wadanda suka dade da barin aiki da wasu kananan hukumomin, amma sunayensu na kan kundin biyan albashin karamar hukumar.” In ji shugabar.
Hajiya Ladi ta kuma ce har yanzu akwai sama da ma’aikata 60 da ba a tantance su ba wadanda har yanzu suna cikin kundin biyan albashin.
Sai dai ta bayyana cewa sabon kundin biyan albashin karamar hukumar zai fito nan ba da dadewa ba.
Shugabar ta kuma bayyana cewa, “Mun yi nisa sosai wajen tantance ma’aikatanmu kuma mun samu dimbin nasarori a kan hakan.”
Hajiya Hadiza ta ce babban abin da ya fi ci musu tuwo-a-kwarya shi ne albashin ma’aikata kuma suna kokarin ganin sunayensu ya shiga cikin kudin biyan albashin karamar hukumar domin biyan albashi a kan lokaci.
“Lokacin da muka zo mun samu harkar tafiyar da ma’aikatan karamar hukumar a tabarbare, don wadanda muka karbi shugabancin daga gare su, sun gaza biyan albashin watanni da dama. Saboda haka ina kira ga ma’aikata da su kara hakuri. Komai zai daidaita ba da dadewa ba.” In ji ta.
Daga karshe, shugabar ta ce, babban burinta shi ne ta ga ta kafa tarihin inganta jin dadin ma’aikatan karamar hukumar wanda zai yi daidai da zamani.
Title :
An Gano Yadda Ake Biyan Matattu Albashi A Kaduna
Description : Shugabar rikon kwarya ta Karamar Hukumar Chikun da ke cikin Jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Ladi Yahuza ta bayyana cewa Karamar Hukumar ta bank...
Rating :
5