Bayanai kwarara daga Industrin KannyWood na alamta cewa soyayya na neman kulluwa tsakanin fitaccen mawakin nan na Hausa da Turanci Dan Kano mazaunin kasar Amurka, Naziru Ahmad Hausawa (Nazirums) da jaruma Nafisat Abdullahi.
Mashkur24 ta samu bayanin cewa tun da dadewa fitaccen mawakin ke dawainiya da soyayyar jarumar fina-finan wanda itama ana ganin akwai hakan a zuciyarta amma basu bayyanawa juna ba.
"Mun zaci jaruman zasu bayyana soyayyarsu a wajen kalankuwar mawaka da Arewa Creative Industry ta shirya a Kaduna washe garin Sallah amma sai abun bai yiwu ba. Amma dai duk wanda ya halarci taron yaga yadda Naziru Hausawa ya hau wasu wakokin soyayya masu sosa zuciya wadanda har sun tsuma jarumar kuma ta gane da ita yake, domin har sai da fitaccen mawakin ya nufo wajen da jarumar Nafisat ke zaune da nufin yin amfani da damar wajen bayyanawa duniya soyayyarsa ga jarumar sai DJ ya kashe wakar aka fara tafi wanda ba mamaki wannan ne ya kashewa jarumin kwarin guiwar aiwatar da manufarsa" inji wani makusancin Nazirums
Kawo yanzu dai jaruma Nafisat Abdullahi bata yi martani akan wannan batu ba tun bayan da ake yadashi haka shima bangaren mawakin bai karyata lamarin ba.
Wannan dai ya nuna gaskiyar cewa Jaruman na shirin kulla soyayya wacce kusan zata dauki hankali a duniyar industry "domin Naziru a shirye yake ya auri jarumar ya tafi da ita cen Amurka" cewar wani na kusa da mawakin wanda ya nemi a sakaye sunanshi
Ya kara da cewa "Kuma ya sha alwashin barin jarumar ta cigaba da sana'arta ta fim muddin tana sha'awar hakan bayan sunyi aure."
Dama dai a kwanakin baya an ruwaito Jarumar na bayyana cewa zata auri wani wanda ba Dan fim ba wanda masu hasashe ke ganin dama komi ka iya sauya "idan Allah yayi sai kaga ansha biki da fitaccen mawakin"
Source Mashkur24
Title :
Akwai Yiwuwar Soyayya Tsakanin Nafisa Abdullahi Da Mawaki Naziru Ahmad Hausawa
Description : Bayanai kwarara daga Industrin KannyWood na alamta cewa soyayya na neman kulluwa tsakanin fitaccen mawakin nan na Hausa da Turanci Dan Kano ...
Rating :
5