Yan majalisar wakilan Najeriya da
gwamnatin Amurka ta zarga da neman karuwai a lokacin da suka je kasar
domin yin wani aiki sun bukaci Amurka ta kawo hujja.
Daya daga
cikinsu, Muhammad Gololo, ya shaida wa BBC cewa babu kanshin gaskiya a
zargin da Amurka ta yi musu, yana mai kalubalantar kasar da ta kawo
hujjar bidiyo ko hutunan da ke nuna cewa sun nemi karuwai a kasar.
Ya kara da cewa a shirye yake ya koma kasar domin kare kansa daga wannan zargi.
A cewarsa, zai kai karar gwamnatin Amurka idan ta gaza bayar da hujjar da ke nuna cewa ya nemi karuwa a kasar.
Ita dai Amurka, a wata wasika da jakadanta a Najeriya Mr. James
Entwistle ya aikewa shugaban majaliasar wakilan, Yakubu Dogara, ta zargi
'yan majalisa uku daga cikin goma da suka kai ziyara kasar da nuna
rashin kamala da yunkurin yin fyade da neman karuwai.
A cewar Mr
Entwistle 'yan majalisar su ne: Mohammed Garba Gololo (APC, Bauchi),
Samuel Ikon (PDP, Akwa Ibom) da kuma Mark Gbillah (APC, Benue).
Ya
kara da cewa Mohammed Garba Gololo ya yi yunkurin rungumar wata
ma'aikaciya da ta je gyara masa dakinsa da zummar yin lalata da ita.
Mr.
Entwistle ya kara da cewa "Mark Terseer Gbillah da Samuel Ikon sun
bukaci ma'aikatan wurin ajiye motoci na otal din da su nemo musu
karuwai."
Source Bbc
Title :
Yan Majalisan Najeria Sun Musanta Neman Karuwai
Description : Yan majalisar wakilan Najeriya da gwamnatin Amurka ta zarga da neman karuwai a lokacin da suka je kasar domin yin wani aiki sun bukaci Amu...
Rating :
5