Daga: Bilya Hamza Dass
Kimanin Watanni Shida kenan tin bayan da rundunar Sojojin kasar Nigeria ta kaddamar da wani tsarraren hari akan Harkar Musulunci a Nigeria a ranakun 12-12-2015 zuwa 14-12-2015 suka afkawa 'Yan'uwa almajiran Sheik Ibrahim Zakzaky da kisan kare dangi.
A yayin harin ta'adancin sun kashe daruruwan mutane ciki akwai maza da mata da yara tare da kona wasu. Sannan sun jikkita wasu dayawa jama'a maza da mata. Yazuwa yanzu munada kididdiga ta mutane 781 wadanda ba'agansuba Wanda hakan yana nuna Imma sun kashe su suka kona ko suka bizne ko kuma suna tsare dasu a wuraren da ba'asaniba.
A wannan ta'anuti da sojoji sukayi sun kashe mata masu ciki da kananan yara, tare da aikata fyade ga wasu matan daga bisani suka kashesu suka kona wasu da ransu domin su boye mummunan barnar da sukayi. Sannan sojojin suka kwashe gawarwakin 'yan'uwa musulman suka bizne a manyan ramuka batare da banbance tsakanin jinsi ko babba da karamiba.
Bayan sun kashe duk Wanda suke a gidan Jagoran Harkar Musulunci Sheik Ibrahim Zakzaky, sojojin sun sojojin sun bude wuta akansa tare da me dakinsa Malama Zeenatudeen Ibrahim daga nan suka tafi dasu zuwa wajan daba'asani kuma suka hana duk wata dama dazata isa zuwa garesu, kama daga 'yan'uwa na dangi, almajiranshi da lauyoyinshi ko likitotinshi har tsawon wata Hudu (4).
Sannan suka rusa gidan Sheik Zakzaky domin rufe munin aikin, bayan kona gidan, suka rusa cibiyar karantarwansa ta Husainiyya tare da Makabartan Shahidai ta Darul-Rahama tare da tone kabarbura dake garin Dambo da Fudiyya Centre da gidan da aka bizne mahaifiyarsa darike duk wani muhalli mallakar harkar musulunci kuma duk wannan rushe rushen karkashin jagorancin gwamnatin jihar Kaduna ne .
Bayan duk faruwan wannan zalunci, tauye hakki da cin zarafi, tare da karan tsaye ga hakkin dan adam, sun kama da Daruruwan 'yan'uwan suna tsare dasu jikinsu akwai masu raunuka annbarsu batare da wani kulawaba. sai kuma gwamnatin jihar Kaduna takafa wata kwamiti dazatayi bincike akan abin dayafaru.
Harkar Musulunci ta kauracewa hukuman binciken saboda bata tsammanin adalci daga hukumar domin hukumar tana dauke da Membobi masu zazzafan kiyayya ga Harkar musulunci da jagoranta, cikinsu akwai Wanda yayita rubutu abaya yananuna harkar musuluncine hadarine da barazana, Wanda har yana Neman tallafin gwamnati datayi amfani da karfi wajan ganin karshen Harkar musulunci a Nigeria. Haka yasa harkar musulunci ta janye daga wannan hukuma ta jeka nayika.
Hukuman tayita gayyato masu tanadadden kiyayya da mumunan nufi zuwa gabanta domin tara hujjoji wajan bayyana Harkar Musulunci a matsayin kungiyan ta'adanci ko kuma sununata amatsayin wata kungiyan da ake daukan nauyinta domin haifar da wata gwamnatin me iko bayan gwamnatin kasa, wanda wannan shine abinda shugaban kasa ya bayyana a matsayin Hujjansa na afkamana, sun bayyana wannan.
Tsawon wannan lokaci suna tsare da jagoran Harkar Musulunci Sheik Ibrahim Zakzaky da Matarsa tare da daruruwan 'Yan'uwa babu wani dalili na gaskiya da ake tuhumansu. Akwai hadari me yawa dayake tattare cikin hakan, amma muna cigaba da daukan matakan hankali da hanyoyin da suka dace domin ganin ansake mana jagoranmu batare da wani Sharadiba kawai abin nema kenan.
Alokaci guda muna sanar da cewa munasane da Daruruwan 'Yan'uwanmu da aka haka babban rami aka rufe a garin Mando har su 347 wanda gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da wannan a gaban hukumar bincike. Dan haka muna kira da abamu ga warwakin Shahidanmu domin yimusu jana'iza kaman yanda Addini yatanadar.
Duk cikarsu sunada Addini da iyalai dan haka sunada bukatan kulawa, dan haka yazama dole a tonosu domin wannan dakuma sanar da muhallin da sauran 'yan'uwammu suke. Kuma bama wajan kariya da kulawa yazama dole domin wajene da aka aikata mummunan aiki, kuma shedane babba.
Harwala yau muna kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta bada kulawa ga 'Yan'uwammu datake tsare dasu akurkuku domin akwai wadanda rayuwarsu take Cikin hadari, na kula da lafiya.
Tsawon wannan watanni ana cigaba da tsare jagoranmu da almajiransa muna kira da a gaggauta Sakeshi kuma abamu dukkanin Muhalinmu tare da biyashi Diyya dakuma hukunta duk me hanu acikin ta'annutin.
Bilya Hamza Dass
Bilyahamzadas@gmail.com
12-06-2016 ( 07-Ramadan 1437)
Title :
Watanni Shida Da Kisan Kiyashin Zariya - Muna Jiran Adalci
Description : Daga: Bilya Hamza Dass Kimanin Watanni Shida kenan tin bayan da rundunar Sojojin kasar Nigeria ta kaddamar da wani tsarraren hari akan Har...
Rating :
5