Fitaccen jarumin nan na fina-finan Kannywood, Adam A. Zango, ya sa wata mata kukan murna a lokacin da ta gan shi.
Wani hoton bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram ya nuna shi a cikin motar da ke tsaye, yana sauraron wata mace sanye da hijabi.
Matar dai, wacce ta ce sunan ta Maryam, ta fashe da kuka da ta ga jarumin.
A cikin kuka ta ce, "Allah ka rage min sonka a raina. Ni ba so nake na aure ka ba, kawai Allah ne ya hada jinina da kai."
Ta bukaci jarumin ya ba ta lambarsa ta waya, kuma ya ba ta, inda shi ma ya karbi tata lambar wayar.
A wani takaitaccen bayani da ya rubuta a kusa da hoton bidiyon, Adam A. Zango ya ce, "Allah Sarki! Ba ta boye irin farin cikin da ya mamaye ta ba lokacin da ta gan ni.
Wadansu ka iya cewa hakan shirme ne ko kauyanci ne, amma a gani na hakan cikakkiyar kauna ce. Na gode wa Allah da ya ba ni irin wadannan masoya."
Mabiyansa da dama sun yi tsokaci a kan bidiyon, inda suka bayyana ra'ayoyin da suka sha bamban a kansa.
Yayin da Zeeagaj ya ce, "Allah Sarki ta bani tausayi. Don Allah Adam ka aure ta domin tana sonka, so na hakika", shi kuwa Muhammad Abdullahi Harun cewa ya yi " Kina wahalar da kanki."
Kusan mutane 8,000 ne suka kalli bidiyon a daidai lokacin da muke rubuta wannan labari.
Ga Video
Domin samun Bidiyoyi Hausa Da Labarai Ziyarci Telebijin
1AREWA TV
Title :
Video: Wata Masoyan Adam A Zango Ta Masa Kuka
Description : Fitaccen jarumin nan na fina-finan Kannywood, Adam A. Zango, ya sa wata mata kukan murna a lokacin da ta gan shi. Wani hoton bidiyo da...
Rating :
5