TAMBAYAR DA TA SANYA MALAMI KUKA
Shehin Malami (Mufti) na kasar Saudia ya fashe da kuka yayin da ya amshi tambayar wani bawan Allah dan kasar Somalia a tashar Talbijin.
Inda ya ke tambayar mene ne ingancin azuminsa idan bai samu abincin da ya yi sahur da shi ba, kuma bai samu na buda baki ba?
Ya kai wanda kake da abinda za ka yi sahur da buda baki, sai yaushe za ka daina korafi ka kuma gode wa Allah akan ni'imar da ya yi maka, ba tare da ka tambaye shi ba, alhali ga wasu can suna daukar Azumi da buda baki ba tare da sun samu abinda za su sanya a baki ba?
Da wannan kuma za ka gane kuskuren masu sanya hotunan abinda suka ci ko suka sha na buda baki a shafukan zumunta na 'facebook', 'instagram', 'whatsapp' da sauransu.
Ya Allah ka yalwatama duk wanda yake cikin kunci, ka yassare wa duk wanda ba shi da shi, ka ba mu arziki ta hanyar halal, ka yi mana me kyau a duniya da lahira.
Title :
Tambayar Da Ta Sanya Sheik Mufti Ismail Menk Kuka
Description : TAMBAYAR DA TA SANYA MALAMI KUKA Shehin Malami (Mufti) na kasar Saudia ya fashe da kuka yayin da ya amshi tambayar wani bawan Allah dan kas...
Rating :
5