Wasu daga cikin marubata tafsiri na baya-baya sun rubuta cewa, Yajuju da Majuju da aka ambata a Alkur’ani, su ne Magul ko Tatar. Wasu ma suka ce, su ne kasashen turawa da Amrika da Rasha da China.
Wannan ra’ayi nasu ba shi da inganci ko kadan, saboda dalilai masu yawa, ga kadan daga ciki kuma a dunkule kamar haka:
1. Wannan ra’ayi ne da ya sabawa Alkur’ani da ingantattun Hadisai na Manzon Allah masu yawa, wadanda suke nuna cewa, bayyanar Yajuju da Majuju za ta kasance ne bayan dawowar Annabi Isa (A.S) da kashe Dujal.
2. Allah ya ba mu labarin cewa, Zul-Karnaini ya gina ganuwa tsakanin Yajuju da Majuju da sauran mutane, ta yadda ba za su iya gauraya da sauran jama’a ba. Yayin da su kuma wadancan kasashen daman can suna tare da jama’a, kuma suna shiga cikin sauran kabilu na duniya, babu wani shamaki a tsakaninsu.
3. Ya tabbata a hadisai cewa, bayan Yajuju da Majuju sun bayyana ba za su dade ba sosai. Yayin da su kuma wadancan kasashe na kafirai daman can suna nan tun jimawa.
4. Ya tabbata a Alkur’ani da Hadisi cewa, ganuwar da Yajuju da Majuju suke bayanta ba za ta rushe ba sai dab da tashin kiyama.
5. Hakanan wannan ra’ayi ya saba wa abin da Zul-Karnaini ya fada na cewa, ganuwar da Zul-Karnaini ya gina tsakanin Yajuju da Majuju da sauran mutane ganuwa ce mai karfin gaske da ba za su iya hauro ta ba, ko su huda ta, sai dab da tashin kiyama.
6. Hadisai ingantattu sun nuna cewa, manyan alamomin tashin kiyama idan suka fara bayyana to, za su ci gaba da bayyana ne a jere-jere ba kakkautawa. Yayin da su wadancan kasashe daman tun can farko ma akwai su, ba daga baya ne suka bayyana ba.
7. Kasashen kafiran nan na duniya daman can akwai su tun kafin zamanin Manzon Allah (S.A.W), amma bai taba cewa su ne Yajuju da Majuju ba. Haka nan babu wani daga cikin sahabbai da ya taba cewa su ne, ko wani dadadden malami.
8. Hadisi ya tabbata cewa, su Yajuju da Majuju idan sun bayyana za su shanye ruwan koramar Tabariyya. Amma su wadancan kasashe na kafirai suna da isasshen ruwan sha, ba su da wata bukata ta su zo su shanye ruwan koramar Tabariyya.
Don haka wancan ra’ayi ra’ayi ne marar tushe marar asali.
Title :
Su Wanene Yajuju Da Majuju - Muhammad Sani R/Lemu
Description : Wasu daga cikin marubata tafsiri na baya-baya sun rubuta cewa, Yajuju da Majuju da aka ambata a Alkur’ani, su ne Magul ko Tatar. Wasu ma su...
Rating :
5