salam
da alama muna da mutane masu
hangen nesa a arewa da na dauka duk
son buhari ya rufe mana ido mun manta
da hukuncin Allah akan shuwagabannin
mu duk wada baya son a gaya ma buhari
gaskiya jahili ne kuma karya yakeyi shi ba
masoyin buhari bane makiyinsa ne. nima
bazan lissafo nawa kadan
1. buhari yana kuskure da dama a mulkinsa amma ga misalinsu mutane suna kwana da yunwa ta dalilin buhari a yanzu rayuwa mai tsada jamaah sukeyi ta dalilinka buhari ka sani Allah zai tambayeka ranan gobe kiyama yaya ka tafiyar da al ummanka.
2. mutane ba kudi a hannunsu idan sunje asibiti ba kudin magani ba aikin da zasuyi su samu kudi kai gashi dan ciwon kunne ne ya dameka ka dauki kudi ka fita kasar waje don jinya da kana da tunani talakawa nawa zaa ciyar da kudin daka fita dashi kasar wajen nan?
3. kace an kwato kudi a hannun barayin gwamnati kudin yana da yawa kuma meyasa bazaka ma al umma aiki da kudin ba kana ta ajiyesu wanda ba amfanan al umma zasuyi ba tunda ajiyesu akayi kawai.
ina kira a gareka shugaban kasa buhari kaji tsoron Allah ka gyara tsarin mulkin ka ko al umma zasu samu sassauci mutane suna cikin wahala da kuncin rayuwa wasu suna bara wasu sun koma sata duk saboda rashin babu. ka duba ka gani har yanzu jammah suna maka adduah amma kai ka dako hanyan da ba daidai bane ka tuna barna akeyinta lokaci daya amma gyara sai a hankali don haka bazaka iya gyara nigeria a shekara hudu ko takwas ba Allah da yayi mu shi zai gyara mu ba kai ba. kaji tsoron Allah
Allah kuma ya baka ikon gyarawa. Amin
bashir ladan yuguda
11 - 06 - 2016
Title :
Shawari Ga Shugaba Kasa Najeriya
Description : salam da alama muna da mutane masu hangen nesa a arewa da na dauka duk son buhari ya rufe mana ido mun manta da hukuncin Allah akan shuw...
Rating :
5