Mataimakin shugaban majalisar dattawa sanata Ike Ekweremadu ya mika takardar koke gaban majalisar dinkin duniya, majalisar dokokin Amurka da tarayyar turai EU dama wasu manyan cibiyoyin kare dimokaradiyya a duniya inda yake koken Buharin na yunkurin yi wa dimokaradiyyar Nijeriya kanshin mutuwa.
Ekweremadu ya ce irin wannan bita da kulli da ake yi wa shugabanni a majalisarsu yunkuri ne na kulle bakin majalisa ta yarda Buhari da 'yan kanzaginsa kadai za su ci karensu babu babbaka.
Ekweremadu ya kara da cewa babancin milkun farar hula da soja majalisa ce kawai wacce da zarar an kulle mata baki shike nan sai a fara kama karya.
A domin haka Madu ke nemen wadannan cibiyoyi da su gaggauta shiga lamarin kafin abubuwa su kara cebewa.
Title :
Sanata Ekweremadu Ya Kai Karar Buhari Majalisar Dinkin Duniya
Description : Mataimakin shugaban majalisar dattawa sanata Ike Ekweremadu ya mika takardar koke gaban majalisar dinkin duniya, majalisar dokokin Amurka d...
Rating :
5