Wasu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun halaka wani yaro dan shekara goma a ciki birnin Kano, bayan sun yi garkuwa da shi a ranar Litinin din da ta gabata. Bincike ya nuna cewa sunan yaron Musa Salisu.
Rahotanni sun nuna cewa an yi garkuwa da marigayin ne da misalin karfe biyu na rana a unguwar Na'ibawa dake cikin birnin Kano.
Wani kawun mamacin mai suna Kafinta Salisu, ya bayyana cewa ba su gano cewa an yi garkuwa da yaron ba har sai bayan awanni uku, inda wani da ba a san ko wanene ba ya kira su ta waya yake sanar da su halin da yaron ya tsainci kansa a ciki.
Ya kara da cewa masu garkuwan sun bukaci da a ba su naira milyan dari biyar kafin su saki yaron, inda ake kokarin sanin hanyar da za a ba su kudin, sannan kuma a gefe daya an sanarwa da hukumar 'yan sanda
Kafinta Salisu ya kara da cewa "bayan mun sake kiran lambar da aka kira mu da ita a washe gari da safe don jin yadda kudin zai shiga hannunsu, sai suka sanar da mu cewa har sun yi wa yaron yankan rago. Suka kuma gaya mana inda suka yar da gawar, wato ta wajen bayan gari.
Kafinta ya kara da cewa tuni suka yi wa yaron jana'iza bayan sun gano gawar, inda aka binne shi a makabartar unguwar Na'ibawa.
A yayin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano DSP Magaji Musa Majia kan lamarin, ya tabbatar da aukuwar hakan, inda ya kara da cewa suna kan gudanar da bincike.
Saidai rundunar 'yan sandan ta ki yi karin haske game da inda aka kwana a batun, amma wata majiya daga 'yan uwan yaron da aka kashe sun tabbatar da kama wasu mutane biyu da ake zargin suna da hannu a kisan.
Title :
Photos: An Halaka Dan Shekara Goma A Kano Bayan An Yi Garkuwa Da Shi
Description : Wasu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun halaka wani yaro dan shekara goma a ciki birnin Kano, bayan sun yi garkuwa da shi ...
Rating :
5