Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dawo gida Nijeriya a yammacin yau bayan tsawon kwanakin da ya yi yana hutu a kasashen Burtaniya da Kwadebuwa.
Bincike ya nuna cewa tsohon shugaban kasar ya dawo gidan ne ta filin jirgin Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Idan ba a mance ba dai, a makon da ya gabata an yi ta yada jita-jitar cewa Jonathan ya gudu ya bar Nijeriya ne don gudun kada a tuhume shi kan badakalar kudin sayen makamai. Inda ya fito ya musanta zargin da ake yi masa.
Title :
Photos: Goodluck Jonathan Ya Dawo Najeriya
Description : Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dawo gida Nijeriya a yammacin yau bayan tsawon kwanakin da ya yi yana hutu a kasashen Burtaniya da...
Rating :
5