Daga Bashir Abdullahi El-Bash
A jiya Laraba ne uwargidan shugaban kasa A'isha Muhammadu Buhari ta samu isowa jihar Bauchi don kawo gudummawar ta ga 'yan gudun hijira da kuma sauran mutane masu karamin karfi a jihar ta Bauchi.
Uwargidan shugaban tace wannan tallafin ta yi ne domun kawo dauki akan halin da jama'a ke ciki
Haka kuma A'isha Buhari ta yi godiya ga mutanen jihar Bauchi akan irin goyon bayan da suke baiwa mijinta, wato Shugaban kasa Muhammadu Buhari
A cikin bayananta ta yabawa Mai Girma Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar bisa ga namijin kokarin da yake yi wurin kawo ci gaba a jihar.
Cikin abubuwan da uwargidan shugaban kasa ta kawo a akwai shinkafa, taliya, yaduna, sabulai da sauransu.
Shi Kuma Mai Girma Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ya yi mata godiya bisa ga zabar jihar don kawo irin wannan tallafin. Ya yi kuma yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu'.
Bugu da kari Gwamnan Mohammed Abdullahi Abubakar ya yi godiya ga Allah bisa ga damar da al'ummar jihar Bauchi suka ba shi. Ya kuma yi godiya ga jama'a bisa ga adduo'in alheri da suke yi wa wannan gwamnanti ta jihar Bauchi
*Amadu manager Bauchi, shine ya turo mana wadannan hotuna daga jihar Bauchi. Daga Rariya
Title :
Photos: A'isha Buhari Ta kaddamar Da Tallafi A Jihar Bauchi
Description : Daga Bashir Abdullahi El-Bash A jiya Laraba ne uwargidan shugaban kasa A'isha Muhammadu Buhari ta samu isowa jihar Bauchi don kawo gud...
Rating :
5