Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni, bayan ya dauki tsawon kwanaki 13 a yawon ganin likita. A lokacin da ya sauka a kasar, ta filin jirgin Nnamdi Azikwe a birnin tarayya Abuja, an tambayi shugaban kasa yanda yake jin jikinsa, ya ce ya samu lafiya har yayi barkwanci ga masu rahoto, cewa su gwada karfi ta hanyar dambe.
Shugaban kasa ya koma bakin aiki a ranar Litinin, 20 ga watan Yuni, ya kuma samu tarba daga mataimakin shugaban ksa, Ferfesa Yemi Osinbajo a Ofishin sa. Mataimakin shugaban kasar ya wakilce sa a taron majalisar tarayya sau biyu, a bayan tafiyar sa.
A da an shirya tafiyar ne na tsawon kwanaki 10. kamar yadda haka tsara zai ga likita gwani a fannin kunne. Duk da haka, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara kwanakin sa a kasar bayan likitocin sa sun bashi shawaran ganin likita a kasar Landan.
A lokacin da yake kasar Landan, shugaban jam’iyyar All Progressive Congress, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da sarkin Ijebu, da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma babban jigon APC, Alhaji Atiku Abubakar ysun ziyarce shi.
Title :
Photos: Buhari A Offishin Sa..Ya Koma Bakin Aikin Sa
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni, bayan ya dauki tsawon kwanaki 13 a yawon ganin likita. A lokacin da...
Rating :
5