A jiya Juma'a ne uwargidan shugaban kasa Hajiya A'isha Buhari ta karbi bakuncin matan tsoffin shugabannin kasar nan wadanda suka hada da Mai Shari'a Fati Abubakar Abdulsalami, Hajiya Hadiza Shagari, Matar Tafawa Balewa, Misis Aguiyi Ironsi , Hajiya Maryam Abacha, Misis Victoria Gowon da kuma Misis Alex Ekweme domin ganawa a fadar shugaban kasa.
Haka kuma matar shugaban majalisar Dattijai, Toyin Saraki da matan gwamnonin jam'iyyar APC, matan manyan hafsoahin sojoji da sauranau suna daga cikin wadanda suka halarci taron.
A yayin zaman uwargidan shugaban kasan ta yi kira ga matan da su taimaka mata da shawarwari a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Sannan kuma ta yi amfani da wanan damar wajen raba littafin da ta rubuta game da rayuwar mata.
Title :
Photos: Aisha Buhari Ta Hada Liyafa Wa Tsoffin Matan Shugabannin Kasar Nan A Villa
Description : A jiya Juma'a ne uwargidan shugaban kasa Hajiya A'isha Buhari ta karbi bakuncin matan tsoffin shugabannin kasar nan wadanda suka ha...
Rating :
5