Manchester United ta kulla yarjejeniyar daukar Eric Bailly, domin ya taka mata- leda idan ya samu takardun izinin zama a Turai.
Eric dan kasar Ivory Coast, zai je Old Tarfford ne kan kudi fam miliyan 30 a kwantiragin shekara hudu.
Bailly dan kwallon Villareal ya yi wasanni 40 a gasar Laliga, guda biyar din farko ya yi su ne a Espanyol.
Dan wasan ya koma taka-leda a Villareal kan kudi fam miliyan hudu da dari hudu a watan Janairun 2015.
Erik ya buga wa Ivory Coast dukkan wasannin da ta lashe na kofin nahiyar Afirka a shekarar 2015 wanda aka yi a Equatorial Guinea.
Title :
Manchester United Ta Siya Eric Bailly
Description : Manchester United ta kulla yarjejeniyar daukar Eric Bailly, domin ya taka mata- leda idan ya samu takardun izinin zama a Turai. Eric dan ka...
Rating :
5