Duk wanda yaga matsala tayi masa yawa ya bincika alakarsa da iyayansa.
Duk wanda yaga baya samun Nasara a duk abinda yasa gaba ya duba alaka da iyayansa .
Duk wanda baya jin dadin rayuwar sa, ya bincika yadda yake zaune da iyayansa
Duk wanda yaga makiya suna rinjaye a kansa, ya tintibi zaman sa da Iyayansa.
Sabawa iyaye yana jawo dukkan matsala a rayuwa
1 Sa iyaye kuka, saboda bakin ciki
2 Yiwa iyaye tsawa, ko hantara ko tsaki ko gunguni
3 Kosawa da iyaye da gajiya da su ko tsanarsu
4 Daurewa iyaye fuska ko sha musu kunu
5 Yiwa iyaye kallon raini da hadarin kaji
6 Yiwa iyaye tsiwa, da daga murya akan su
7 Kushe iyaye, da daukar su gidadawa.
8 Kauda kai, idan iyaye suna magana .
9 Fifita mata akan iyaye
10 Fifita Abokai akan iyaye
11 Jawowa iyaye matsaloli da rigingimu
12 Gulmar iyaye
13 Zagin iyaye ko jawo musu zagi
14 Damun kiyaye da kade kade da wake wake
15 Rashin shawara da iyaye
16 Kauracewa iyaye
17 Tsagalgalewa iyaye da rashin kunya
18 Iyaye su dinka tsoran dan su
19 Kin amfani da sunan iyaye
20 Dukkan iyaye da gajiya da su
21 Fatan mutuwar su
22 Yi musu gori dan kayi wani abu.
23 Boyewa iyaye samu, ko wadata,
24 yiwa iyaye karya
25 Karyata iyaye
26 Yiwa iyaye sata,
27 YI musu gori
28 YI musu musu,
29 Rashin yi musu addua
30 Barin iyaye cikin kunci da wahala.
Allah kasa mu gama da iyayanmu lafiya, kayi musu rahma kamar yadda suka yi mana tarbiyya tun muna Yara.
Title :
Mai Sabawa Iyaye Kayi Kuka Da Kanka - Mal.Aminu Ibrahim Daurawa
Description : Duk wanda yaga matsala tayi masa yawa ya bincika alakarsa da iyayansa. Duk wanda yaga baya samun Nasara a duk abinda yasa gaba ya duba al...
Rating :
5