Assalamu alaikum malam ina maka fatan alkhairi abin da kakeyi na taimakon al umma ALLAH ya saka maka da alkhairi, malam ni dai na kasance na aikata kuskure dan kuwa na aikata istimnai ban san adadi ba. duk sanda abin ya motsa min wani gida nake shiga ni kadai na kulle.. nayi nadamar wannan aiki nawa sakamakon fadakarwar da nake ji, sbd ni gani nake danaje nayi zina fa ashe shima babban laifine nayi nadama danaji fadakarwa akan hakan, kuma malam lokacin da nake wannan aiki ina neman aure har ma ankusa auren baifi sati biyu ba wannan nadama ta sameni to malam babban abinda yake damu na shine na hadu da daukewar sha'awa gaba daya ga matata saboda anyi auren amma kuma idan ina tare da ita kamar namiji nake tare dashi dan kuwa bana jin sha,awa ko kadan kuma koda natara da ita ahaka bana jin wani dadi, malam ataimaka min ya zanyi wajen tuba ALLAH ya yafe min? malam kuma ataimakeni da magani, malam aboye sunana.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Shi wannan al'amari na Istimna'i ba Qaramar chutarwa yake yiwa jikin Dan Adam ba. Domin kuwa bayan chutarwar da yake yiwa jikin Mutum, to yana mutukar chutar da Zuciyar 'Dan Adam din ma.
Mun sha yin wa'azi anan Zauren Fiqhu dangane da wannan sha'anin. Kuma mun gaya muku illolinsa na fili da na boye.
Daukewar sha'awa tana daga cikin matsalolin da Istimna'i yake haifarwa, Kuma ana maganceshi ne ta hanyoyi kamar haka:
1. Kayi kokari ka tuba sosai daga wannan aikin. Ka yawaita Istighfari, ka Kaurace ma harkar baki dayanta.
2. Ka yawaita shan ruwan Inabi da kuma Kankana. Domin kowanne daga cikinsu yana kunshe da sinadarai masu Qarfi wadanda zasu dawo maka da sha'awarka, Kuma zasu karfafa maka kuzarinka.
3. Ka samu Garin Habbatus Sauda cokali 1, garin Habbur Rashad shima haka, Sannan garin Kanumfari rabin cokali. Ka hadasu acikin Madara mai dumi. Sannan ka sanya zuma aciki ka raba biyu. Kasha safe da yamma. in sha Allahu zaka samu waraka.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU (07-06-2016) 02-RAMADHAN 1437.
Title :
Maganin Daukewar Sha'awa
Description : Assalamu alaikum malam ina maka fatan alkhairi abin da kakeyi na taimakon al umma ALLAH ya saka maka da alkhairi, malam ni dai na kasance na...
Rating :
5