Daga Abubakar Hamza Zakariyya Misau,
lallai mafarkin kowani Xa namiji dangane da aure ko samun matar da zai yi rayuwa da ita, bai wuce, Ya samu matar da zai samu nitsuwa da ita, wacce take sonsa, ta kuma damu da shi, mai bashi kulawa a ko da yaushe.
Kuma lallai idan Mutane suka nazarci ayoyin Alqur'ani mai karimci da hadisan Annabi (صلى الله عليه وسلم) za su ga cewa lallai NASSOSHIN sun yi bayanin sifofin MACE TAGARI; abar neman MASU HANKALI, da cewa itacemai sifar: RIQO da addini, da qoqarin baiwa Allah haqqoqinsa da kuma miji, Haka kuma sun nuna cewa itace: Saliha, mai xa'a, bayan kasancewarta Musulma, ko Mumina. Mace tagari ta kan zama mai gaskiya, da haquri, mai sallah, da azumi, da sadaka ko zakka, mai yawan ambaton Allah, tare da yin biyayya wa mijinta, da kiyaye farji daga alfasha, da kuma kiyaye dukiyar mijinta daga tozartawa, da kuma iyalansa. Har wani hadisin ya nuna cewa, Mace ba za ta lazimci waxannan aiyukan ba face ta shiga aljannar Ubangijinta, a indaAnnabi (صلى الله عليه وسلم) yake cewa:
"إِذَا صَلَّتِ الْمَرْأَةُ خَمْسَهَا، وَصَامَتْ شَهْرَهَا، وَحَفِظَتْ فَرْجَهَا، وَأَطَاعَتْ زَوْجَهَا، قِيلَ لَهَا: ادْخُلِي الْجَنَّةَ مِنْ أَيِّ أَبْوَابِ الْجَنَّةِ شِئْتِ".
Ma'ana: "Idan Mace ta yi sallolinta guda biyar, ta yi azumin watanta guda xaya, ta kuma kiyaye farjinta, sannan ta yi biyayya wa mijinta, Sai ace da ita: Ki shiga aljanna daga qofar da kika ga dama daga cikin qofofin aljannah" [Musnad Ahmad, lamba: 1661, Hadisi ne, hasan].
Kuma don qoqarin taqaicewa Mutane sifofin Macen da tafi alkhairi Wassu masu hikima da ilimi sun dunqule sifofin irin wannan matar cikin maganganunsu taqaitattu masu fasaha.
Kamar yadda suka yi bayanin wacece asharariyar Mace,
Xaya daga cikinsu yana cewa:
1) Itace: Take yardar da Ubangijinta (تُرضي ربَّها).
2) Take kuma shagwavar da Mijinta (تُدلِّل زوجَها).
3) Kuma bata barin zaman gidanta (لا تفارق بيتَها).
4) Kuma tana yin sallolinta guda biyar (تصلِّي خمسَها).
5) Kuma bata fitar da sirrinta (لا تُخْرِج سِرَّها).
6) Kuma ba a ganin takalminta (لا يُرى نَعلُها).
7) Kuma ba a jin sautinta (لا يُسمَع صوتُها).
8) Kuma ba a sanin siffarta (لا يُعْرَفُ وصفُها).
9) Mai izza a cikinMutanenta (العزيزة في قومها).
10) Mai jin qasqanci a karan-kanta (الذليلة في نفسها).
11) Ga xanta qarami; Mai shayar da shi ne, Mai rarrashinsa (لوليدها مرضعةٌ حانيةٌ).
12) Gidanta kuma aljanna ce, da abin tsinkanta suke a kusa (بيتها جنَّة دانية).
13) Idan ta samu wani alkhairi daga Mijinta sai ta yi godiya (إنْ وجَدَت مِن زوجها خيرًا شكَرَتْ).
14) Idan kuma ta ga wani sharri a wurinsa sai ta yi haquri (وإنْ رأَتْ منه شرًّا صبَرَتْ).
15) Idan kuma ya shigo wurinta sai ta yi farin ciki tana murmushi (إنْ دخَل عليها سُرَّت وتبسَّمَتْ).
16) Idan kuma ya fita daga gidanta sai ta yi baqin ciki, tana yin bege (إنْ خرَج مِنْ بيتِها حزِنَتْ وتشوَّقَتْ).
17) Idan yayi fushi da ita sai ta jure ta yi haquri (إنْ غضِب منها تحمَّلَتْ وتحلَّمَتْ).
18) Idan ta fiskanto shi sai ta burge shi (إنْ أَقْبَلَتْ عليه أعْجَبَتْه).
19) Idan kuma baya tare da ita to sai ta kiyaye shi (إنْ غاب عنها حفِظَتْه).
20) Idan ta ga aibinsa sai ta voye (إنْ رأَتْ عَيْبَه ستَرَتْه).
21) Idan ya nemi ta yi masa uzuri sai ta karvi uzurinsa (إنْ اعتذر منها عَذَرَتْه).
Da aka tambaye shi kuma, Wacece mai sharri a cikin Mata, Sai yace:
1. Itace: Mai yawaita rashin lafiya (الممراض).
2. Mai yawaita haila (المحياض).
3. Wacce take kuka ba tare da sababi ba (التي تبكِي مِن غيرسبب).
4. Mai kuma yin dariya ba tare da an samu abinda yake sanya al'ajabi ba (وتضحكُ مِن غير عجب).
5. Idan zata fita sai ta yi ado, ta kuma bubbuxe jiki (إنْ خرَجَتْ تبرَّجَتْ وتكشَّفَتْ).
6. Idan kuma ta shiga; sai ta yankwane, ta bubbushe (إنْ دخَلَتْ ذبُلَتْ وتقشَّفَتْ).
7. Maganarta mai ciyo ne (كلامُها وعيد).
8. Sautinta kuma mai tsanani ne (وصوتُها شديد).
9. Tana bubbune kyawawa (تدْفَنُ الحسنات).
10. Sai kuma ta riqa yaxa munana (وتُفْشِي السيئات).
11. Kuma bata yin haquri akan musibu (ولا تَصْبِر على النكبات).
12. Tana ta makon zamani akan Mijinta (تعينُ الزمانَ على زوجها).
13. Shi kuma, Bata taimakonsa akan zamanin (ولا تُعِينُه على الزمان).
14. Idan ya shiga, sai ta fita (إنْ دخَل خرَجَتْ).
15. Idan kuma ya fita, sai ta shiga (وإنْ خَرَجَ دخَلَتْ).
16. Idan ya kusance ta sai ta gudu (إنْ قَرَبَها نفَرَتْ).
17. Kuma, ga abokin zamanta (miji) Mai butulci ne (ولعشيرها كفَرَتْ).
18. Kuma idan ta yi fushi sai ta yi fajirci (إذا غضِبَتْ فجَرَتْ).
19. Xanta a koyaushe yana cikin yunwa (طفلُها جائع).
20. Farillarta kuma, abar tozartawa ce (وفرضُها ضائع).
21. Ubangijinta yana Mai fushi (ربُّها غضبانُ).
22. Shi kuma Mijinta, yana ta nadama (وزوجُها ندْمانُ).
23. Kuma "Shexan" yana sonta (ويحبُّها الشيطانُ).
24. Tana kai kuka, alhalin itace Mai zalunci (تشتكِي وهيَ ظالمةٌ).
25. Tana yin shaida, alhalin bata wurin (وتشهَد وهي غائبةٌ).
26. Tana kuma yin zargi alhalin itace mai aibin (وتذُمُّ وهي عائبةٌ).
27. Harshenta yana da tsayi (لسانُها طويلٌ).
28. Tufanta kuma, gajere ne (وثوبُها قصيرٌ).
29. Shi kumagidanta, tana qaurace masa (وبيتُها هجير).
30. Zancenta qarya ne (قولُها زورٌ).
31. Shi kuma hawayenta na fajirci ne (ودمعُها فُجُور).
32. An jarrabe ta da, azabar rami, da tavewa (ابتُلِيَت بالويل والثبور).
33. Da kumamanya-manyan al'amura (وعظائم الأمور).
[Duba littafin / Almustaxraf fi kulli fannin Mustazraf, shafi 463-464].
Ni da Ku gabaxaya; Allah ta'alah ya azurta mu, da mafi alherin Mata, Ya kuma tsare mu daga sharrinsu.
Title :
Macen Da Ta Fi Alheri Da Wadda Ta Fi Sharri
Description : Daga Abubakar Hamza Zakariyya Misau, lallai mafarkin kowani Xa namiji dangane da aure ko samun matar da zai yi rayuwa da ita, bai wuce, Ya...
Rating :
5