Wata kotu a Misra ta yanke wa zababben Shugaban Kasar a karkashin jam'iyyar Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi, Mohammed Morsi hukuncin daurin rai da rai.
Tun da farko dai kotun ta wanke shi daga laifin cin amanar kasar na samar da bayanan sirri ga kasar Katar inda a maimakon haka aka same shi da laifin jagorantar haramtacciyar kungiya.
Title :
Kotun Misra Ta Yanke Wa Morsi Hukuncin Daurin Rai Da Rai
Description : Wata kotu a Misra ta yanke wa zababben Shugaban Kasar a karkashin jam'iyyar Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi, Mohammed Morsi hukuncin daur...
Rating :
5