Tsohuwar Abokiyar Aikinsu, Fati Sulaiman Na Neman Tallafi
Ita dai Fati Sulaiman fitacciyar jarumar finafinan Hausa ce wadda ta jima da yin aure. Mun samu labari cewa ta na fama da ciwon daji (cancer) na mahaifa, har ta kai mahaifar na zubar da ruwa. Likitoci sun ce tilas ne a cire mahaifar don a ceci ran ta.
To, Fati da maigidan ta ba su da halin biyan kudin. Abin da ake bukata shi ne N200,000 kacal.
Yanzu ne ya kamata 'yan fim da masoyan su su nuna halacci, su nuna cewa su ma 'ya'ya ne, su taimaka wa wannan baiwar Allah. A gaskiya, mutum daya ma ya na iya biyan wannan kudin idan akwai niyyar. Idan 'yan fim su ka ga dama, za su iya tara mata ko miliyan 2 ake bukata, ba dubu dari 2 kacal ba.
Akwai wani fitaccen jarumi wanda lokacin da gwamnatin Shekarau ta kulle shi ita Fatin ce ta rika kai masa abinci a gidan yari safe da rana da dare. Wannan alama ce ta irin halaccin ta. Kuma duk wani sha'ani na 'yar fim kamar bikin aure ko suna Fati na halarta. Wallahi wannan jarumin zai iya bada N200k din nan a yau din nan idan ya ga dama!
Saboda haka dai ya kamata 'yan fim su yi hobbasa su agaza wa Fati Sulaiman don kaunar su ga Manzo (SAW), don alfarmar wannan wata na Ramadan.
Mu tuna, irin wannan ibtila'in yana iya fadawa kan kowa.
Idan ka karanta wannan sako, KA TURA WA ABOKAN KA DA FOLLOWERS DIN KA, sannan kuma ka kawo taka gudunmawar don Allah. Kuma gudunmawa ba ta kadan.
Title :
Kalubale Ga Yan Fim Din Hausa
Description : Tsohuwar Abokiyar Aikinsu, Fati Sulaiman Na Neman Tallafi Ita dai Fati Sulaiman fitacciyar jarumar finafinan Hausa ce wadda ta jima da yin...
Rating :
5