Zlatan Ibrahimovic ya bayar da tabbacin cewar zai buga wa Manchester United tamaula a kakar wasan bana.
Yarjejeniyar Ibrahimovic mai shekara 34, za ta kare da ne Paris St-Germain wadda ya buga wa wasanni tsawon shekara hudu.
Dan wasan zai murza-leda a Old Trafford karkashin Jose Mourinho, wanda ya horar da shi a Inter Milan.
Ibrahimovic ya rubuta a shafinsa na Instagram cewar, "Lokaci ya yi da zan sanarwa duniya cewar Manchester United zan buga wa tamaula.''
United wadda ta kare a mataki na biyar a kan teburin gasar Premier da aka kammala ba ta ce komai kan batun ba.
Title :
Ibrahimovic Zai Koma Club Din Manchester United
Description : Zlatan Ibrahimovic ya bayar da tabbacin cewar zai buga wa Manchester United tamaula a kakar wasan bana. Yarjejeniyar Ibrahimovic mai shekar...
Rating :
5