Daga Jarida Rariya
* An sake rufe hedkwatar jam'iyyar
A wani taron gaggawa da gwamnonin PDP suka yi a yau Alhamis a Abuja sun yanke shawarar yanke duk wata hulda da Shuugaban Jam'iyyar, Modu Sheriff.
Gwamnonin sun nuna cewa Modu na da wata manufa ta daban wadda ta ci karo da yunkurin da ake yi na farfado da jam'iyyar don tunkarar zaben kujerar gwamnan Edo da za a yi kwanan nan.
Haka nan kuma, a karo na biyu Shugaban Kwamitin Amintattu na PDP, Jibril Wali ya sake rufe hedkwatar jam'iyyar bayan arangama a tsakanin magoya bayan Modu Sheriff da 'na 'ya'yan kwamitin riko.
Title :
Gwamnonin PDP Sun Nesanta Kansu Da Modu Sheriff
Description : Daga Jarida Rariya * An sake rufe hedkwatar jam'iyyar A wani taron gaggawa da gwamnonin PDP suka yi a yau Alhamis a Abuja sun yanke s...
Rating :
5