Gwamnatin Tarayya na farin cikin sanar da ku shirin N-Power, tsarin da zai taimaka wajen gane marasa aikin yi, basirar su da irin taimakon da gwamnati ya kamata ta yi musu.
Tsarin na N-Power zai taimaka wajen samarwa matasan da suka kammala da wadanda ma ba su kammala ba ayyukan yi. Tsarin zai koyarwa matasa sana'o'i kala daban - daban.
Daukar farko a shirin na N-Power zai fi bada fifiko kan ilimi, noma, fasaha, gine - ginen zamani da kuma ayyukan hannu.
Tsarin N-Power na shirya Nijeriya ne yadda za ta fita kasashen duniya don yin tafiya kafada da kafada da manyan kasashe wajen samun kudaden shiga da bunkasa asusun tattalin arzikin mu na duniya.
Wannan ba karamar dama ba ce ga 'yan Nijeriya, musamman wadanda suka kammala karatu ko kuma suke da basira kuma har yanzu babu aikin yi.
Wannan shafi na Aso Rock Villa zai ci gaba da kawo muku yadda shirin yake tafiya lokaci-lokaci don ba ku damar fahimtarsa sosai.
Za ku iya ziyarar shafin www.npower.gov.ng don karin bayani kan yadda za a ci moriyar tsarin.
Title :
Gwamnatin Tarayya Ta Soma Yunkurin Samar Da Ayyukan Yi
Description : Gwamnatin Tarayya na farin cikin sanar da ku shirin N-Power, tsarin da zai taimaka wajen gane marasa aikin yi, basirar su da irin taimakon ...
Rating :
5