Gwamnatin jihar Lagos da ke kudancin Najeriya ta rufe majami'u 70 da masallatai 20 da kuma wasu gidajen shakatawa 11.
Hukumar kula da muhalli ta jihar ta ce ta dauki wannan mataki ne domin rage yawan sauti da karar da ke fitowa daga wuraren ibadar wadanda kan damu al'umma.
Gwamnatin Lagos ta ce an samu nasarar rage kashi 35 ne kadai daga cikin kashi 100 na yawan sautin da ake damun al'umma da shi a wuraren ibada.
Amma gwamnatin ta ce tana son rage amon sauti a majami'u da masallatai da wani kaso mafi cancanta a wuraren ibada, kafin shekara ta 2020.
Tuni dai gwamnatin jihar ta bullo da tsarin da wuraren ibadar za su bi yadda sautin da kan fito daga amsa-kuwwa ba zai dinga damun mutane ba.
Yawanci majami'u kan gudanar da ibada a yayin da dare ya tsala ne da kuma masallatai wadanda ke yin kiran Sallah da kuma wa'azi kafin ko bayan salloli biyar.
Gwamnatin jihar dai ta ce ba za ta ce komai ba kan cigaban da wannan mataki ya kawo, amma mutanen da ke makwabtaka da majami'u da masallatai za su bai wa kansu amsa a kan hakan.
Wakilin BBC ya zanta da wani mutum da ke makwabtaka da irin wadannan wuraren ibada, inda ya ce, ''Hakan ya shafe ni, in ka kasance mabiyin addini ba ana nufin za ka yi abinda ka ga dama gaba gadi ba. In an ce majami'u ko masallatai na damun mutane na goyi baya in an nemi su rage karfin sautin da ke fitowa.''
Jihar Lagos ta hana nuna tsiraici
Sai dai wasu jagororin mabiya addinan biyu sun shaida wa BBC cewa, idan batun sauti mai takura wa al'ummar gari ake to ba abu ne da za a dora wa wuraren ibada laifi ba.
Shugaban hukumar kula da muhalli ya ce suna samun hadin kai daga masallatai da sau da yawa bayan kulle su da kuma sake bude su, su kan bi umarnin hukuma wajen rage sautin.
Gwamnatin jihar dai ta ce za ta ci gaba da aniyar da ta daura na rage sautin a wuraren ibada.
Hukumar kula da muhallin ta ce daga yanzu ba za ta bari ana kafa wuraren ibada barkatai ba, musamman yadda ake killace wasu dakuna ko kango da sunan wajen yin ibada.
A bara ma dai gwamnatin jihar ta kulle wuraren ibada da ta zarge su da tsananta amfani da amsa-kuwwa da kuma addu'o'i na kiyamullaili da mabiya addinin Kirista kan yi idan dare ya yi dare.
Title :
Gwamnatin Legas Ta Rufi Coci 70 Da Masallatai 20
Description : Gwamnatin jihar Lagos da ke kudancin Najeriya ta rufe majami'u 70 da masallatai 20 da kuma wasu gidajen shakatawa 11. Hukumar kula da m...
Rating :
5