Duk da cewa a baya gwamnatin tarayya ta nuna rashin gamsuwar da duk wani mataki da zai iya shafar darajar kudin Nijeriya wajen hadar chanji da ragowar kudaden kasashen duniya a baya da alama babban bankin Nijeriya zai chanja tsarinsa na hada-hada da Naira.
Wannan bayani na fitowa ne daga jaridar #Wall_Street ta kasar Birtaniya inda Buhari da kansa ya sanar da haka duk da cewa ba ai cikakken bayani kan tsarin ba.
Dama a baya anyi
wa gwamnati Nijeriya tayin rage darajar kudin kasar kasantuwar faduwar darajar man fetir da Nijeriya ta dogara da shi don samun kudin waje wanda hakan yasa darajar takardar kudi ta Naira ta fadi wanwar.
Baya bayan nan ne gwamnati taki yarda da matakin ina take cewa bata samu gamsassan bayanai ba don rage darajar ta Naira, duk da cew masana tattalin arziki sun nunawa gwamnati alfanu hakan a yayin da kasarnan ke fama da matsalar tattalin arziki.
Title :
Gwamnatin Buhari Ta Yarda Da Sabon Tsarin Hada-Hada Da Naira
Description : Duk da cewa a baya gwamnatin tarayya ta nuna rashin gamsuwar da duk wani mataki da zai iya shafar darajar kudin Nijeriya wajen hadar chanji...
Rating :
5