Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya shiga yajin aiki a wani mataki na tausaya wa ma'aikatan jihar wadanda a halin yanzu ke yajin aiki bisa rashin biyansu albashi har na tsawon watanni biyar.
A wani jawabi da ya yi wa al'ummar jihar, Fayose ya nuna cewa bai da kudin da zai iya biyan albashi saboda kudaden da jihar ke samu daga asusun tarayya ya ragu matuka. Ya ci gaba da cewa, shi ma ya shiga yajin aikin ne don jajanatawa iyalan ma'aikatan.
Title :
Gwamnan Jihar Ekiti Ya Fara Yajin Aiki
Description : Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya shiga yajin aiki a wani mataki na tausaya wa ma'aikatan jihar wadanda a halin yanzu ke yajin aiki bisa...
Rating :
5