Daga Rariya
Rahotanni daga Amurka na cewa mutane hamsin ne suka hallaka a yayin da wani dan bindiga ya bude wuta kan jama’a a wata mashaya da masu auren jini ke taruwa a birnin Florida na Orlando.
'Yan sandan Orlando sun bayyana cewa tuni dan bindigar ya bude wuta a wani gidan rawa na pulse da ke tsakiyar birnin ya mutu a musayar wuta da 'yan sanda , kuma a cewar tashoshin talabijin na CBS da NBC tuni aka tantance mutum da sunan Omar Mateen dan Amurka amma dan asalin kasar Afganistan.
Ko baya ga wadanda suka hallaka a musayar wuta mutane 53 da suka jikkata Kamar yadda magajin birnin Buddy Dyer ya sanar.
Kawo yanzu dai humomin yankin sun ce babu wata barazana, aman saboda yadda hankula jama’a suka tashi, magajin birnin ya bukaci gwamnan Florida daya ayyana dokar ta baci.
Tuni dai Hukumar FBI ta budda bincike kan ayyukan ta’adanci domin sanin mutumin ya aikata hakan ne kashin kan sa ko kuma ya samu umarni daga wajen kasar.
Title :
Dan Bindiga Ya Hallaka Mutane Hamsin A Birnin Orlandon Dake Amurka
Description : Daga Rariya Rahotanni daga Amurka na cewa mutane hamsin ne suka hallaka a yayin da wani dan bindiga ya bude wuta kan jama’a a wata mashaya...
Rating :
5