Tsohon gwamnan Kano kuma jigo a PDP Malam Shekarau ya bayyana cewa Buhari da APC sun ci amanar talaka domin kawo yanzu talaka bai ga Chanji da aka yi masa alkawari ba.
Shekarau ya bayyana haka ne a yau yayin da yake kaddamar da kwamitin mutum 44 da aka kafa don farfado da ruhin PDP jiya a Kano.
Shekarau yace duk da cewa an nemi talaka ya zabi chanji karkashin Buhari, Shekarau ya kara da cewa, to amma talaka bai ga komai ba sai mugun talauci, yunwa, fatara, da wahalar man fetir.
Shekarau ya nemi da talaka ya dage don jarraba jam'iyyarsu ta PDP don ganin Chanjin da talaka yake nema.
Title :
Buhari Ya Yaudari Yan Najeriya - Shekarau
Description : Tsohon gwamnan Kano kuma jigo a PDP Malam Shekarau ya bayyana cewa Buhari da APC sun ci amanar talaka domin kawo yanzu talaka bai ga Chanji ...
Rating :
5